Ancelotti ya ce zai ritaya amma...

Carlos Ancelotti
Image caption Ancelott kocin Real Madrid

Mai yiwuwa Carlos Ancelotti ya yi ritaya daga horar da 'yan wasa da zarar wa'adinsa a real Madrid ya kare.

Anceloti ya koma Madrid ne daga PSG, bayan ya sanya hannu a kan wata yarjejeniya ta shekaru uku da suka cimma da kungiyar ta Madrid, wadda ta lashe Gasar cin Kofin Zakarun Turai har sau tara.

Kocin ya shaida wa Sky Sport Italia cewa, "Sau da yawa ana tambaya ta ko zan yi kocin Roma ko tawagar Italiya nan gaba? Na kan amsa da cewa ban sani ba, watakila na yi ritaya bayan na gama kocin Madrid".

Ancelotti, mai shekaru 54, ya yi wasa a Roma da AC Milan kafin ya zama mai horar da 'yan wasa.

Kafin zuwansa Real Madrid ya yi kocin AC Milan da Chelsea da PSG.