Za a nuna Bundesliga a kasashe da dama

Germany Bundesliga
Image caption Bundesliga za ta yi gogayya da Premier da Laliga

Gasar Jamus ta Bundesliga ta cimma yarjejeniya kwantiragin nuna gasar a fadin duniya.

Tun daga shekarar 2015 zuwa 2016, kamfanin 21 Century Fox ya soma nuna gasar Bundesliga a arewaci da kudancin Amurka da yawancin nahiyar Asiya a tsawon shekaru biyar.

Haka kuma za a nuna gasar a kasashen Italiya da Holland da Belgium a tsawon shekaru biyu.

Shugaban gasar Bundesliga, Christian Seifert ya ce "Cimma yarjejeniyar na haska yadda gasar Bundesliga za ta zama hajja a wasanni na duniya.