Ghana za ta kara da Masar

Ghana Black Stars
Image caption Birnin Kumasi zai karbi gagarumin wasa

Ghana za ta karbi bakuncin Masar ranar Talata a zagayen farko na wasan neman gurbi a Gasar cin Kofin Duniya da za a yi a Brazil a shekara ta 2014.

Karawar da za su yi sau biyu, za ta kayatar matuka ganin a tsakaninsu za a fitar da wacce za ta wakilci nahiyar Afirka a Brazil badi.

Masar ce kadai da ta samu nasarar wasanninta gaba daya a wasan neman cancantar shiga gasar ta duniya.

Sai dai ba a da tabbacin zagaye na biyu ko za su kara a Alkahira, domin FIFA ta nemi Masar ta tanadi tsaro ga tawagar Ghana kafin 19 ga watan Nuwamba.