Najeriya za ta kara da Italiya

Super Eagles  Nigeria
Image caption Nijeriya ta fara jiyo kanshin Brazil

Najeriya za ta kara da Italiya a wasan sada zumunci na kwallon kafa a filin Fulham da ke Landan ranar 18 ga watan Nuwamba.

Wasan da Najeriyar za ta kara da zakarun Kofin Duniya karo hudu, za a yi shi ne bayan kwana biyu da wasan Najeriyar da Ethiopia karo na biyu na neman zuwa gasar Kofin Duniya.

Najeriyar wadda ta lashe wasan farko da ci 2-1 ranar Lahadi, tana sa ran sake nasara ta biyu ranar 16 ga watan Nuwamba a Calabar.

Super Eagles din na fatan karawar da zasu yi da Italiya, za ta zamo shirye shiryen tunkarar gasar Kofin Duniya a Brazil.