Igiebor ya sami rauni a Habasha

Super Eagles attacked
Image caption An kai mana hari da manyan duwatsu

Dan kwallon Nigeria Nosa Igiebor ya samu rauni a ranar Lahadi, lokacin da aka kaiwa motarsu hari, bayan buga wasan cancantar shiga gasar cin kofin duniya da Habasha.

Dan wasan tsakiya na Real Betis ya nemi taimakon gaggawa bisa raunin da ya samu a tafin hannunsa, lokacin da aka farfasa tagogin motar da suke ciki, a lokacin da suke barin filin wasa na Addis Ababa.

Najeriya dai ta samu nasara a kan Habasha da ci 2-1, a wasan.

Mataimakin shugaban kwallon kafa na Najeriya, Mike Umeh ya shaida wa BBC ce wa "Muna fata FIFA za ta dauki matakin da ya dace."