Ingila za ta kara da Chile da Jamus

England National Team
Image caption Tawagar Ingila a kokarin ta na tunkarar kofin duniya

Ingila za ta fafata da Chile da kuma Jamus a wasan sada zumunci a filin wasa na Wembly, a cikin shirye-shiryenta na tunkara Gasar cin kofin duniya.

Ingila dai ta casa Poland da ci 2-0, sannan ta samu tikitin shiga kofin duniya.

Za ta fara gwabza wa da Chile ne ranar 15 ga watan Nuwamba, sannan ta fafata da Jamus wadanda suka taba zama zakarun kofin duniya sau uku, kwana hudu bayan wasan da za su yi da Chile.

Rabon Ingila ta kara da Jamus tun lokacin da aka casa ta da ci 4-1 a wasan zagaye na biyu na Gasar cin kocin duniya a shekarar 2010.

Wasannin za su zamo cikon wasannin da Ingila ta kara a Wembley da kasashen Brazil da Ireland da Scotland a bukukuwan cika shekaru 50 da kafa hukumar kwallon kafar kasar.