FIFA: Spain ce ta farko a duniya

Image caption Shugaban Fifa, Sepp Blatter

Hukumar kwallon kafa ta duniya-Fifa ta fitar da sabon jerin karfin kasashe a fagen kwallon kafa a duniya.

Jerin ya nuna cewar har yanzu kasar Spain ce ta farko a duniya sai Jamus ta biyu a yayinda Argentina take matakin na uku.

A nahiyar Afrika, Ivory Coast ce ta farko amma kuma ta 17 a duniya sai Ghana wacce ke ta biyu amma ta 23 a duniya.

Algeria ce ta uku a Afrika sai Najeriya wacce take ta hudu a nahiyar amma kuma ta 33 a duniya.

Jerin kasashe 10 na farko:

1. Spain 2. Germany 3. Argentina 4. Colombia 5. Belgium 6. Uruguay 7. Switzerland 8. Netherlands 8. Italy 10.England

Karin bayani