Hitzfeld zai yi ritaya bayan kofin duniya

Kocin Switzerland Ottmar Hitzfeld ya sanar da cewa zai yi ritaya, bayan kammala gasar cin kofin duniya da Brazil za ta karbi bakunci, a shekarar 2014.  Hitzfeld mai shekaru 64 na daga cikin masu horar da 'yan wasa hudu da suka lashe kofin zakarun Turai, a kungiyoyi biyu daban-daban, ya kuma taimakawa Switzerland ta dare matsayi na 7, a jerin kasashen da suka fi iya kwallo da FIFA ta fitar.  Sanarwar na zuwa ne a lokacin da aka tabbatar da Switzerland, cikin kasahen gaba guda takwas da za su fara buga wasa a gasar cin kofin duniya.  Ya jagoranci Switzerland zuwa gasar cin kofin duniya karo na biyu, ya kuma zamo zakaran rukuni na biyar, ya lashe wasanni bakwai, ya yi canjaras uku a cikin wasanni 10 da ya kara, inda ya kasance a saman rukunin kasashen Iceland da Slovenia da Norway da Albania da Cyprus.
Image caption Ottmar Hitzfeld ya yi kocin Borussia da Bayern Munich

Kocin Switzerland Ottmar Hitzfeld ya sanar da cewa zai yi ritaya, bayan kammala gasar cin kofin duniya da Brazil za ta karbi bakunci, a shekarar 2014.

Hitzfeld mai shekaru 64 na daga cikin masu horar da 'yan wasa hudu da suka lashe kofin zakarun Turai, a kungiyoyi biyu daban-daban, ya kuma taimakawa Switzerland ta dare matsayi na 7, a jerin kasashen da suka fi iya kwallo da FIFA ta fitar.

Sanarwar na zuwa ne a lokacin da aka tabbatar da Switzerland, cikin kasahen gaba guda takwas da za su fara buga wasa a gasar cin kofin duniya.

Ya jagoranci Switzerland zuwa gasar cin kofin duniya karo na biyu, ya kuma zamo zakaran rukuni na biyar, ya lashe wasanni bakwai, ya yi canjaras uku a cikin wasanni 10 da ya kara, inda ya kasance a saman rukunin kasashen Iceland da Slovenia da Norway da Albania da Cyprus.