Zambiya: Fifa ta hukunta TP Mazembe

Zambia National Team
Image caption Tawagar 'yan kwallon Zambiya

Hukumar kwallon kafa ta Zambiya na neman Fifa ta dauki mataki a kan kulab din TP Mazembe, sakamakon hana 'yan wasanta uku halartar wasan sada zumunci tsakanin kasar da Brazil a China.

Zakarun kofin Africa a shekarar 2012 sun yi rashin nasara a hannun Brazil daci 2-0, amma 'yan wasanta uku masu rauni ba su buga mata ba, da suka hada da Nathan Sinkala da Rainford Kalaba da Stoppila Sunzu.

Mataimakin shugaban hukumar kwallon kasar Boniface Mwamelo yace"ya kamata a dauki mataki don kaucewa faruwar haka nan gaba".

Mazembe ta karyata zargin cewa ta ki barin 'yan wasan su yi tafiya tare da sauran tawagar kasar Zambiya.