Low ya sabunta kwangilarsa a Jamus

Image caption Joachim Low

Kocin Jamus, Joachim Low ya sabunta kwangilarsa na karin shekaru biyu masu zuwa.

Dan shekaru 53, ya maye gurbin Jurgen Klinsmann a shekara ta 2006, kuma zai ci gaba da jan ragamar tawagar 'yan kwallon kasar zuwa shekara ta 2016.

Janar Manaja Oliver Bierhoff da kuma mai horadda gola Andreas Kopke, suma sun sabunta kwangilarsu.

A karkashin jagorancin Low, Jamus ta sha kasa a wasan karshe na gasar cin kofin kasashen Turai a shekara ta 2008, sannan kuma Spain ta doke su a wasan kusada karshe a gasar cin kofin duniya a shekara ta 2010.

Karin bayani