Al-Ahly da Pitares wasan karshe

Al-Ahly of Egypt
Image caption Al-Ahly nada kofin bakwai, Pirates nada guda daya

Al-Ahly na kan hanyar kare kofin zakarun nahiyar Afrika bayan da ta doke Coton Sports ta Kamaru a dukan daga kai sai mai tsaron raga ta samu zuwa wasan karshe.

An tashi wasa 1-1 aka buga daga kai sai mai tsaron raga, Al-Ahly ta lashe wasa da ci 7-6 a wasan da suka kara a Red Sea Resort dake El- Gouna.

Kafin wannan wasa sun tashi wasa 1-1 a wasan da suka buga a Kamaru.

Al-Ahly zata kara da Orlando Pirates a wasan karshe, da zasu fafata gida da waje a watan gobe.