Ferdinand da Hodgson sun shiga FA

Ferdinand
Image caption Ingila na shirin ganin ta taka rawar gani a Brazil

An zabi tsohon kaftin din Ingila Rio Ferdinand da koci Roy Hodson cikin hukumar kwallon kafa don inganta kungiyar kwallon kafar kasar.

Nadin ya zo kwana daya da Heather Rabbatts mace tilo cikin hukumar kwallon kafar ta soki nadin mambobin hukumar da cewa dukkansu farar fata ne kuma maza zalla.

Kocin Ingila Hodson mai shekarau 66, ya sama wa Ingila gurbin buga gasar kofin duniya da za a kara a Brazil.

Ferdinand mai shekaru 34, ya bar buga wa Ingila kwallo a watan Mayu bayan da ya buga wasansa na 81 a watan yulin shekara ta 2011.