Rashin kokarinmu 'yan wasa ne — Moyes

David Moyes
Image caption 'Yan wasa ya kamata su tashi tsaye

Kocin Manchester United David Moyes ya musanta ikirarin da ake wa kungiyar mai rike da kofin Premier cewa an dena tsoronta tun lokacin da Sir Alex Ferguson ya bar kungiyar.

An bai wa United tazarar maki takwas tsakaninta da Arsenal, wadda ita ce ta daya a teburin Premier, bayan da suka tashi wasa 1-1 da Southampton a filin wasa na Old Trafford ranar Asabar da ta gabata.

Moyes ya ce"Sir Alex Ferguson ya bar tarihi kuma kwarewarsa za ta iya taimaka wa kowace kungiya a kodayaushe, amma 'yan wasa ne ke nuna tsoronso a cikin filin wasa".

United ta sami nasara a wasa daya kacal daga cikin wasanni hudu a gasar Premier a filin Old Trafford tun lokacin da Freguson ya yi ritaya. Moyes ya ce 'yan wasa ya kamata jama'a su nemi yunkurawarsu domin ci gaban kungiyar.