Flamini ba zai buga wasan B.Dortmund

Arsenal Flamini
Image caption Dan wasan zai yi jinyar rauni

Dan kwallon Arsenal, Mathieu Flamini ba zai buka karawar da kungiyarsa za ta yi da Borussia Dortmund a gasar kofin zakarun Turai ranar Talata ba.

Mai shekaru 29, ya gamu da buguwa a kafarsa, lokacin da suka casa Norwich City da ci 4-1 a ranar Asabar data gabata.

Haka kuma Theo Walcott ya samu koma baya a samun saukin raunin da yake fama da shi a kasan mararsa, shima ba zai buga wasa ba.

Sauran 'yan wasa da suke jinya sun hada da Yaya Sanogo da Lukas Podolski da Alex Oxlade-Chamberlain da kuma Abou Diaby.