Faransa ta gayyaci jakadan Amurka

Image caption Ministan harkokin wajen Faransa, Laurent Fabius

Ma'aikatar hulda da kasashen wajen Faransa ta gayyaci jakadan Amurka a birnin Paris, domin ya amsa tambayoyi dangane da zargin da wata jaridar Faransa tayi cewa, hukumar tsaron kasa ta Amurkan ta nadi miliyoyin maganganu ta waya da jama'a ke yi a Faransa.

Jaridar mai suna Le Monde ta ambato bayanan da Edward Snowden ya kwaramta dake nuna cewa, Amurka ta nadi bayanai fiye da miliyan saba'in ta waya da Faransawa suka yi cikin kwanaki talatin na farkon wannan shekarar.

Jaridar ta Le Monde tayi zargin cewa, bayanai ta waya na Faransawa da Amurka ta nada ba wai kawai na wadanda ake zargi da alaka da ta'addanci, an kuma nadi bayanan wayoyin wasu manyan 'yan siyasa da kuma 'yan kasuwa.

Piraministan Faransa yace, wannan lamari yayi matukar ba shi mamaki.

Karin bayani