Totti zai yi jinyar rauni

Francesco Totti
Image caption Dan wasan ya ce yawan shekaru ba zai hana shi kwallo ba

Kaftin din Roma Francesco Totti zai yi jinyar raunin da ya samu a cinyarsa, lokacin da suka kara da Napoli suka lashe wasan daci 2-0 ranar Jumma a data gabata.

An fidda Totti, daga fili a minti na 33, aka kuma masa gwaje gwaje da dama da nufin sanin munin raunin.

Mai shekaru 37 yana ganiyarsa a kakar wasan bana, ya zura kwallaye uku ya taimaka aka zura kwallaye shida a wasanni takwas da ya buga wa Roma wasa.

Roma za ta yi tattaki ta kara da Udinese a ranar Lahadi mai zuwa.