United za ta iya lashe gasa - Wenger

Image caption Arsene Wenger

Manajan Arsenal Arsene Wenger, yaki yarda a kan cewar Manchester United ba za ta iya lashe gasar Premier ta bana ba.

Gunners ne a saman jadawalin gasar, inda ta baiwa United tazarar maki takwas.

Rawar United a bana itace mafi muni da kungiyar ta taka ciki fiye da shekaru 24, kuma itace ta takwas.

Wenger yace "Shin United ba sa cikin masu kokarin lashe gasar? a'a don za su iya kukakn kura".

Tun lokacin da Sir Alex Ferguson ya yi ritaya ake tababar kamun ludayin David Moyes da ya maye gurbinsa.

Karin bayani