Jeffrey zai gaje ni - Blatter

Sep Blatter
Image caption Shugaban Fifa Sepp Blatter

Shugaban Fifa Sepp Blatter, ya yi nunin cewa Jeffrey Webb zai iya maye gurbinsa a shugabancin kwallon kafa ta duniya a nan gaba.

Webb, mataimakin shugaban Fifa, kuma shugaban hukumar kwallon kafa ta Arewaci da Tsakiyar Amurka da yankin Caribbean wato Concacaf.

Jawabin Blatter a taron karawa juna sa ni a kan kwallon kafa, ya sake haskaka yadda shugaban baya fatan Michel Platini shugaban kwallon kafar Turai ya gaje shi.

Blatter mai shekaru 77, ya fara jagorantar Fifa tun shekara ta 1998.