FA na tuhumar Mourinho kan da'a

Image caption Jose Mourinho

Hukumar kwallon Ingila FA, na tuhumar manajan Chelsea Jose Mourinho bisa saba ka'ida a lokacin wasansu da Cardiff a ranar Asabar.

Alkalin wasa, Anthony Taylor ya umurci Mourinho ya koma wajen 'yan kallo saboda korafi game da bata lokacin da yake zargin 'yan Cardiff na yi.

FA na sauraron Mourinho ya kare kansa, daga nan zuwa karfe shida na yamma a ranar 24 ga watan Okotoba.

Mourinho ya ce "komawa wajen 'yan kallo babu dadi saboda ba zaka iya ganawa da 'yan wasa ba".

Karin bayani