Na kagu na kara da Madrid, in ji Neymar

Neymar barcelona
Image caption Neymar dan kwallon Brazil da Barcelona

Dan kwallon Barcelona, Neymar, yana murnar zai kara da Real Madrid ranar Asabar.

Dan kasar Brazil ya koma Barca daga Santos kan kudi kimanin fam miliyan 48.

Dan wasan, mai shekaru 21 a duniya, ya shaida wa shafin intanet na kungiyar cewa, "Karawa tsakanin Barcelona da Madrid tana da muhimmaci matuka. Wasa ne da ko wanne dan wasa zai so ya buga, kuma dan wasan ya nuna kwarewarsa."

Ya kara da cewa, "wannan shi ne karo na farko da zan fafata a irin wannan wasa; kuma ina fatan wasan ya yi kyau, watau mu samu nasara''.