Bale zai buga wasa da Barcelona

Gareth Bale
Image caption Gareth Bale yayi fama da jinyar raunuka.

Gareth Bale ya shirya karawa da Barcelona ranar Asabar mai zuwa in ji kocin Madrid Carlo Ancelotti.

Bale, mai shekaru 24, yana fama da jinyar wasu raunuka tun lokacin da Madrid ta sayo shi dan kwallon da ya fi tsada daga Tottenham.

"Ya buga wasan da kulab dinsa ya yi da Juventus a gasar cin kofin zakarun Turai, amma zai iya buga wasa a Nou camp" in ji Ancelotti.

Dan wales ya zura kwallo a wasan farko da ya buga wa Madrid a lokacin da suka kara da Villareal ranar 14 ga watan Satumba, amma rauni ya hana shi buga sauran wasannin.

Bale ya fi so ya buga wasa ta bangaren hagu kuma a bangaren za mu sa shi ya buga kwallo.