"Ferguson bai yi wa Gerard adalci ba"

Steven Gerrard
Image caption Steven Gerrard dan kwallon Ingila da Liverpool

Kocin Liverpool ya kare Kyaftin dinsa Steven Gerrard a kan sukan da Sir Alex Ferguson yayi masa cewa dan wasan ba babban dan kwallo bane.

Tsohon manajan Manchester United Ferguson shi ne yayi ikirarin a littafin da ya wallafa, amma Brendan Rodgers ya ce sukan babu adalci a cikinsa.

"I na tunanin kowa ya karanta zargin zai ce yayi tsauri da yawa," inji Rodgers.

Gerrard ya zagoranci Ingila samun gurbin gasar Kofin Duniya a wannan watan.

Tsohon kocin Swansea Rodgers, wanda ya koma Liverpool a 2012 ya kara da ce wa, "na kalli wasannin Gerrard shekaru da dama na tabbata babban dan wasa ne, amma sai ka yi aiki tare da dan wasan zaka gane cewa kwararren dan wasa ne a ko wane yanayi."