Wata takwas keshi ba albashi

Steven Keshi
Image caption Keshi na kokawa da rashin biyan albashi

Kocin Nigeriya Stephen Keshi ya zargi hukumar kwallon kafa ta kasar da rashin biyan sa albashin watanni bakwai.

Keshi, da yake shirye - shiryen karawa da Ethiopia a wasan zagaye na biyu a neman shiga kofin duniya, rabonsa da albashi tun lokacin da ya jagoranci kasar lashe kofin Afrika a watan Janairu.

Keshi ya shedawa BBC ce wa koma bayan da ya samu a rayuwar aikinsa shine rashin biyansa albashin watanni takwas, "ban taba tsintar kaina a wannan yana yin ba".

Tsohon kocin Togo da Mali ya taba shedawa BBC a watan Yulin da ya gabata cewa yana bin bashin albashinsa.

Kuma wannan ba shine karon farko da ba a biyan kociyoyin ba, Christian Chukwu da Shaibu Amodu da Samson Siasia da Austin Eguavoen da John Obuh da Eucharia Uche duk sun koka a baya kan biyan bashin albashinsu.