Toure:'Alkalin wasan bai cancanta ba'

Image caption Yaya Toure ya fusata a kan nuna masa bambamci

Alkalin wasan da ya jagoranci karawar da aka yi tsakanin Manchester City da CSKA Moscow, bai cancanci alkalancin wasa ba, saboda kasa magance kalaman wariyar launin fata.

Shugaban kungiyar dake yaki da wariyar launin fata a kwallon kafa 'Kick it out', Lord Ouseley shine ya bayyana haka, bayan da dan wasan City, Yaya Toure ya kai kara wajen alkalin wasa Ovidiu Hategan a kan cewar ana masa batanci lokacin wasan.

Ouseley yace "alkalin wasan ya gaza a aikinsa, kuma dole ne Uefa ta hukunta shi".

A karkashin dokar Uefa, alkalin wasa nada ikon hana kalaman wariyar launin fata, inda zai iya dakatar da wasa ya bukaci a bada sanarwa a cikin filin wasa kan cewar masu yi su daina.

Tuni kungiyar Manchester City ta aikewa Uefa takardar koke a rubuce a kan korafin nunawa Toure bambamci.

Karin bayani