'Ina jin dadin kwallo a karkashin Moyes'

Image caption Wayne Rooney

Dan kwallon Manchester United, Wayne Rooney ya ce yana jin dadin rayuwa a karkashin sabon manajan kulob din David Moyes.

Dan wasan Ingilan ya nemi barin United bayan rashin jituwa tsakaninsa da tsohon kocinsa Sir Alex Ferguson, wanda a yanzu yayi ritaya.

Ferguson a littafin rayuwarsa da ya kaddamar ya soki Rooney.

Rooney wanda ya cika 28 a ranar Alhamis ya ce bai kara haduwa da Ferguson ba tunda tsohon kocin ya yi ritaya a karshen kakar wasan da ta wuce.

Karin bayani