Zamu iya kauracewa gasar 2018 - Toure

Image caption Yaya Toure

Dan kwallon Manchester City, Yaya Toure ya ce 'yan wasa bakar fata zasu iya kauracewa gasar cin kofin duniya da za ayi a Rasha a shekara ta 2018, idan har kasar bata magance matsalar nuna wariyar launin fata ba.

Dan wasan Ivory Coast din yace " idan bamu da kwarin gwiwa a kan gasar cin kofin duniya to ba zamu je Rasha ba".

Hukumar Uefa na binciken korafin da Toure ya yi a kan cewar magoya bayan kungiyar CSKA sun yi masa kalama batanci a wasansu na gasar zakarun Turai a ranar Laraba a Moscow.

Kungiyar CSKA dai ta musanta cewar an yi masa kalaman batanci.

Idan har aka samu kungiyar CSKA ta laifi, tabbas Uefa za ta hukunta kulob din.

Karin bayani