Sunderland ta doke Newcastle

Kungiyar Sunderland ta doke Newcastle da ci 2 -1 a gasar premier wasan sati na tara, nasarar farko da kungiyar ta samu a gasar bana.

Dan wasan Sunderland Fabio Borini, shine ya zura kwallon da ya baiwa kungiyar samun maki uku, wanda ya taimakawa mata yin sama daga matsayi na karshe a teburin Premier.

Sunderland ta fara zura kwallo ta hannun Steven Fletcher, bayan minti na biyar da fara kwallo, a inda Newcastle ta farke kwallo ta hannun Mathieu Debuchy.

Borini, da ya shigo wasa daga baya, ya buga kwallo tun daga yadi na 25 ta kuma fada ragar Newcastle.

Nasarar da kungiyar ta samu, yasa ta koma matsayi na 19 a teburin Premier da maki 4 kacal.