"Ba sai na gaisa da Mourinho ba"

Manuel Pellegrini
Image caption Pellegrini ya ce ya kamata su sami maki a gidan Chelsea

Kocin Manchester City ya ki gaisawa da kocin Chelsea Jose Mourinho bayan rashin nasarar da su kayi a hannun kungiyar da ci 2-1 a karshen mako.

Lokacin da Fernando Torres ya zura kwallo ta biyu dab da tashi daga wasa, Mourinho cikin murna ya shiga cikin 'yan kallo.

Pellegrini ya ce "Da ma ban yi tsammanin zai aikata abinda yafi haka ba, babu wani abin damuwa."

Mourinho ya maida martani ce wa "Idan suna ganin nayi kuskure, ina neman afuwa."

Mourinho ya kare kansa da cewa ya shiga 'yan kallo ne domin ganawa da dansa da yake baya a zaune.

Kocin ya kara da cewa; "an shiga rudanin daf da a tashi wasa, muka zura musu kwallo a raga.