An fara binciken Scotland da Croatia

fifa
Image caption Fifa za ta dauki matakan hana tada hayaki a filin wasa

Kwamitin ladabtarwa na Fifa ya fara sauraron korafi akan hukumomin kwallon Scotland da Croatia, akan 'yan kallon su da suka kunna hayaki a gasar neman zuwa kofin duniya a filin Hampden Park da ke Glasgow.

Satin da ya gabata kwamitin ya fara binciken hukumomin kwallon Ingila da Poland akan 'yan kallo da suka kunna hayaki a wasan neman shiga gasar kofin duniya a Wembly.

Magoya bayan Croatia sun kunna hayaki a karawar da sukayi a rukunin farko, wanda Scotland ta lashe wasa da ci 2-0.

Koda yake Croatia keda alhakin hada kayayyakin hayakin, Scotland na fuskantar daukar matakin Fifa, saboda ita ce ke da alhakin tsaro.