Gareth Bale na takarar ballon d'Or

Gareth Bale
Image caption Gareth Bale

Dan wasan da yafi tsada a duniya Gareth Bale na cikin mutane 23 da hukumar kwallon kafa ta duniya Fifa ta ware domin lashe gasar fitaccen dan wasa ta bana.

Dan wasan Wales Bale, 24, ya zura kwallaye 26 a Tottenham a bara kafin komawa Real Madrid.

'Yan wasan Premier biyar da suka hada da Eden Hazard, Mesut Ozil, Luis Suarez, Yaya Toure da Robin van Persie ne suka samu shiga cikin rukunin wadanda za su iya cin kyautar ta Ballon d'Or.

Lionel Messi na Barcelona kuma na shirin kare kambunsa a karo na hudu a jere.

Sauran 'yan Barcelona da ke cikin jerin sun hada da Andres Iniesta, Neymar, da Xavi yayinda Christiano Ronaldo ya samu shiga daga Real Madrid.

Bayern Munich wacce ta lashe kofin zakarun Turai a bara na da 'yan wasa shida a cikin jerin da suka hada da Muller, Neuer, Ribery, Robben, Schweinsteiger, da Lahm.