Waye gwarzon koci na duniya?

Jupp Heynckes
Image caption Jupp Heynckes

Tsohon kocin Bayern Munich, Jupp Heynckes, wanda ya jagoranci kungiyar ta lashe kofin Bundesliga, kofin Jamus da kuma kofin zakarun Turai na cikin jerin masu horarwa 10 da hukumar Fifa ta bayyana sunayensu a takarar gasar fitaccen koci ta bana.

Haka kuma tsohon kocin Manchester United Sir Alex Ferguson, kocin Arsenal Arsene Wenger, kocin Chelsea Jose Mourinho da kocin Napoli Rafael Benitez na cikin wadanda aka bayyana sunansu domin lashe gasar.

Benitez ne ya jagoranci Chelsea ta dau kofin Europa a bara kafin komawa Napoli yayinda Mourinho ya maye gurbinsa bayanda ya kasa cin kofin La Liga da na zakarun Turai a Real Madrid.

Sauran sun hada da Carlo Ancelloti na Real Madrid, Antonio Conte na Juventus, Vicente Del Bosque na Spain, da Luiz Felipe Scolari na Brazil.

A ranar 13 ga Janairu 2014 za'a bayyana kocin da ya lashe gasar a Zurich, Switzerland.