"Dole Blatter ya daina raina Ronaldo"

Cristiano Ronaldo
Image caption Madrid bata ji dadin batun da Blatter ya yi a kan Ronaldo ba

Kocin Real Madrid Carlo Ancelotti ya goyi bayan kiran da shugaban kungiyar Florentino Perez ya yi ga shugaban Fifa Sepp Blatter ya janye batun da ya yi akan Cristiano Ronaldo.

Blatter ya danganta Ronaldo da Messi a inda ya ce "Daya yafi tsada ta wajen gyaran gashi."

"Na amince dari bisa dari da maganar da shugabanmu ya yi", inji Ancelotti.

"Mun turawa da Fifa takardar sako, ya janye maganar da yayi, da muke ganin an kaskanta kwararren dan wasa."

Ancelotti ya kara da ce wa har yanzu bai tattauna da Ronaldo ba akan maganar Blatter, amma dan wasan yayi atisaye sosai, kamar yadda ya saba a kullun.

"Kullun yana nuna cewa shi kwararren dan wasa ne, wanda kowa ke girmamawa, kuma ya kamata ya ci gaba da halayyarsa." inji Ancelotti.