Yaya Toure dan Afrika tilo a ballon d'Or

Yaya Toure
Image caption Dan wasan yana fatan lashe kyautar bana

Dan kwallon Ivory Coast da Manchester City Yaya Toure shi ne dan wasa daga Afrika tilo a cikin 'yan wasa 23 da Fifa ta ware domin lashe gasar fitaccen dan wasa ta bana.

Hakan ya na nuna makomar kwallon Afrika da kuma rashin ci gaban kungiyoyin nahiyar Afrika.

A gasar wasan cin kofin duniya da suka gabata, musamman wacce aka kara a Afrika ta kudu a shekara ta 2010 a inda aka samu kasashe shida da suka wakilci nahiyar, kasa daya ce ta kai wasan zagaye na biyu, sauran kasashen suka kasa tabuka rawar gani.

Rashin kokarin nahiyar Afrika na rura zargin cewa har yanzu Africa da sauranta a harkar kwallon kafa.