"Balotelli ba zai bar AC Milan ba"

Balotelli Ac Milan
Image caption Dan kwallon AC Milan Mario Ballotelli

Kocin AC Milan Massimiliano Allegri ya karyata rahotan cewar Mario Balotelli zai iya barin kungiyar a watan Janairu.

Dan kwallon mai shekaru 23, wanda ya koma AC Milan daga Manchester City a watan Janairu, ana rade-radin zai koma Chelsea.

Balotelli da kwantaraginsa zai kare da AC Milan a watan Yuli na shekara ta 2017, ya zura kwallaye 3 a gasar Serie A ta bana.

Allegri ya sanar a shafin internet na kungiyar cewa "hakika ba zai bar kungiyar a watan Janairu ba.

An dakatar da Balotelli wasanni uku a watan Satumba bisa samunsa da laifin amfani da kalamun cin mutunci ga alkalin wasa a karawar da suka yi da Napoli suka kuma lashe wasan da ci 2-1.