Beckham zai kafa kulob a Miami

david_beckham
Image caption David Beckham

Tsohon kyaftin din kwallon kafa na England, David Beckham zai kafa wata sabuwar kungiyar kwallon kafa a garin Miami na Amurka.

Tsohon dan wasan na Manchester United da Real Madrid na neman masu zuba jarin daruruwan miliyoyin daloli domin kafa kungiyar.

Yanzu haka dai kungiyoyin kwallon kafa 19 ne a kasashen Amurka da Canada ke cikin rukunin MLS.

Sai dai rukunin na neman kara adadin kungiyoyin zuwa 24 nan da shekarar 2020.

David Beckham, daya daga cikin 'yan kwallon kafa mafiya shahara a zamaninsa, ya yi ritaya ne a watan Mayun bana bayan da ya bugawa kungiyar PSG ta Faransa wasanni 10.