Uefa ta hukunta CSKA Moscow

Yaya Toure
Image caption Dan kwallon Manchester City da ya shigar da korafi

Hukumar kula da kwallon kafa ta Turai, Uefa, ta ba da umarnin rufe wani bangare na filin wasan kungiyar CSKA Moscow, yayin wasan da za ta kara na cin kofin zakarun Turai na gaba.

Hukuncin ya biyo bayan kalaman nuna wariya ne da aka yi wa dan kwallon Manchester City Yaya Toure.

An tuhumi kungiyar ta Rasha ce, bayan da Toure ya shigar da korafin cewa an furta masa kalaman, a wasan da City ta doke ta da ci 2-1 ranar 23 ga watan Oktoba.

Za a rufe bangaren ne na filin Khimki, a lokacin da CSKA za ta karbi bakuncin zakarun bana Bayern Munich ranar 27 ga watan Nuwamba.

CSKA ta karyata zargin da Toure ya yi na cewa anyi masa kalaman wariya.

Ita dai Uefa ta hukunta kungiyar ce bayan da kwamitin ladabtarwar hukumar ya yi wani zaman sauraren bahasi a Switzerland.