Pantilimon zai maye gurbin Hart a gola

Hart Pantilimon
Image caption Mancity na tararrabin kwazon Hart a bana

Golan Manchester City na fuskantar rasa gurbinsa a hannun Costel Pantilimon, idan yayi kokari a wasan da za su kara da Newcastle a kofin Capital One Cup inji tsohon golan City Joe Corrigan.

Kuskuren da Hart yayi a karawar da suka yi da Chelsea ta baiwa Fernando Torres damar zura musu kwallon da aka lashe su 2-1 a ranar Lahadi da ta gabata.

Corrigan ya shedawa BBC ce wa "A kwai gasar Kofin Capital One ina tunanin Pantilimon zai kama gola, watakila manajan City na san gwada dan wasan, idan yayi kokari ya maye gurbin Hart."

Pantilimon dan Romaniya, mai shekaru 26 ya shiga Manchester City a shekarar 2011 amma bai taba karawa a gasar Premier ba.