Dante ya dawo atisaye a Bayern Munich

dante
Image caption Dante ya dawo Atisaye bayan jinya da ya sha

Kocin Bayern Munich, Pep Guardiola, ya samu labarin da ya karfafa masa gwiwa, tun da kwararren dan wasansa Dante ya koma atisaye, bayan da ya daina buga wasa a sakamakon raunin da ya samu.

Dnte, dan kwallon Brazil mai shekaru 30, ya ji rauni a sawunsa ne lokacin da kungiya ta samu nasara a kan Mainz, makonni biyu da suka wuce, kuma tun a lokacin ya daina buga wasa.

Dante bai buga karawar da kungiyarsa ta yi da Hertha Berlin da gasar kofin zakarun Turai da suka kara da Viktoria Plzen, amma kocni zai iya sa shi a karawar da kungiyar za ta yi da Hoffenheim a karshen sati, bayan da ya dawo atisaye a jiya.

Dan wasan mai tsaron baya ya zamo jigo a kungiyar tun lokacin da aka sayo shi daga Borussia Monchengladbach a shekara ta 2012, ya kuma buga wasanni 15 a wasanni daban- daban.