Wa zai kama gola a Man City ran sati ?

Pantilimon Mancity Goalkeeper
Image caption Golan City da koci ya yabawa a gasar Capital One

Kocin Manchester City Manuel Pellegrini bai yanke golan da zai kama masa raga ranar Asabar ba a gasar Premier da za ta kara da Norwich bayan da Pantilimon ya yi bajinta ranar Laraba da suka cinye Newcastle.

Pantilimon ya hana kwallo shiga zare har karo biyu, lokacin da City ta lashe wasan kofin Capital One da ci 2-0, wasa tilo da suka lashe cikin wasanni bakwai da ba a zura mata kwallo a raga ba.

Joe Hart golan City da Ingila ya yi kura-kurai da dama a kakar wasan bana.

Pellegrini ya ce "duk golan da ya samu damar kama wasa zai samu goyon baya na." Ya kara da cewa "Costel ya fi karawa a wasan Capital One da kofin kalu bale kuma wasanni ne masu mahimmaci a gare shi."

Da aka matsa masa da tambayar makomar Hart, Pellegrini ya amsa da ce wa "na fada muku yau zan yi tunani akan batun."