Tottenham ta kwaci kan ta 8-7 daga Hull

Tottenham
Image caption Tottenham

Tottenham ta kwaci kan ta da kyar a hannun Hull City da ci 8-7 bayan bugun fenariti, inda ta samu kai wa matakin daf da na kusa da na karshe a gasar cin kofin Capital One.

Bayan da kowacce daga bangarorin biyu ta barar da fenariti guda, golan Tottenham Brad Friedel ya kade kwallon da Ahmed Elmohamady na Hull ya buga, abin da ya ba ta nasara a wasan.

An dai kammala miniti 90 na farko kowacce na da 1-1 yayinda aka tashi 2-2 a karshen karin lokaci.

Gylfi Sigurdsson ne ya fara jefa kwallo a raga kafin Freidel ya ci gida. Bayan karin lokaci ne Paul McShane ya kara kwallo daya kafin Harry Kane na Tottenham ya farke.