Martinez ya damu a kan raunin Kone

Image caption Arouna Kone

Kocin Everton Roberto Martinez ya nuna damuwa game da raunin da dan kwallon Ivory Coast Arouna Kone yake fama dashi a idon sawunsa.

Dan wasan mai shekaru 29 ya samu raunin a wasansu da Hull a ranar 19 ga watan Okotoba.

A cewar Martinez, bai san tsawon lokacin da Kone zai shafa yana jinya ba.

Kone ya koma Everton daga Wigan a kan fan miliyan 6 a farkon kakar wasa ta bana, amma rauni ya tilasta masa daina wasa a kwanakinnan.

Karin bayani