Maki daya tsakanin Barca da Atl.Madrid

Diego Costa
Image caption Dan kwallon yana da kwallaye 13 a kakar bana

Kwallon Diego Costa ta 13 a kakar wasan bana, da ya zura a karawar da suka yi da Atletico Bilbao, ta kai Atletico Madrid tazarar maki daya tsakaninta da Barcelona, ta baiwa Real Madrid tazarar maki biyar.

Kwallon da ya zura da ya samu ta hannun David Villa, ta baiwa kungiyar damar lashe wasanni 11 daga cikin wasanni 12 da suka kara.

Coster yana kankan-kan da Cristiano Ronaldo, wajen yawan zura kwallo a raga, kowannensu ya zura kwallaye 13.

An baiwa dan kwallon Bilbao Erik Moran jan kati a minti na 78 a wasan.

Valencia ce kungiya ta karshe da ta lashe kofin La Liga a shekara ta 2004, da ba Real Madrid ko Barcelona ba.

Sai kuma Villareal a shekara ta 2008 data zamo ta biyu a teburi, Real Madrid ta lashe kofi Barcelona ta zame ta uku.