"Joe Hart ya na bukatar hutu"

Hart Pantilimon
Image caption Hart da Pantilimon a filin atisaye

Kocin Manchester City Manuel Pellegrini ya kare hukuncin da ya dauka bayan da ya ajiye Joe Hart a benci ranar Asabar lokacin da sukayi laga-laga da Norwich City, ya ce golan Ingila yana bukatar hutuwa.

An ajiye Hart, mai shekaru 26 a benci, kuma Costel Pantilimon ya maye gurbinsa a wasan da suka lashe da ci 7-0 a filin wasa na Ettihad.

Pellegrini ya sanarwa da BBC cewa "Hart na bukatar hutu kuma hakan zai taimaka masa.

Sai dai tsohon mai tsaron ragar Ingila Ray Clemence ya ce da zan so Pellegrini ya yi hakuri na dan lokaci.