"Messi bai damu da rashin zura kwallo "

Lionel Messi
Image caption Messi ya zura kwallaye da dama a raga

Lionel Messi bai damu da rashin zura kwallo a raga ba, bayan da ya kasa zura kwallo a wasanni hudu da ya yi a gasar La Liga inji kocin Barcelona Gerardo Martino.

Alex Sanchez shine ya zura kwallo a wasan da Barca ta doke Espanyol da ci 1-0 ranar Jumma'a, ta tsawaita yawan lashe wasanni 12 a kakar wasan bana.

Wannan shine karon farko tun watan Agustan shekara ta 2011 rabon Messi ya buga wasanni hudu a jere bai zura kwallo a raga ba.

Martimo ya ce "rashin zura kwallo bai damu Messi ba, ya dade yana zura kwallaye shi yasa idan bai zura ba ake ganin matsala ce."

Duk da rashin zura kwallonsa a La Liga ya zura kwallo a ragar Milan a wasan da su ka tashi 1-1 a gasar cin kofin zakarun Turai.

Messi ya zura kwallaye 223 a cikin wasanni 217 da ya bugawa Barcelona wasanni.