Pirates da Al Ahly sai anje Masar

Al Ahly
Image caption Wasa na biyu zai tantance zakaran bana

Mai masaukin baki Orlando Pirates ta farke kwallo da kyar da gumin goshi, daf da za a tashi wasan da suka kara da Al Ahly aka tashi wasa 1-1, a wasan karshe na cin kofin zakarun Nahiyar Afrika.

Mohamed Aboutrika dan kwallon Al Ahly, shi ya fara zura kwallo a minti na 14.

Mai masaukin baki Pirates ta karbi yawancin taka kwallo a wasan, kuma sai daf da za a tashi ta samu farke kwallo ta hannun dan wasanta Thabo Matlaba.

Pirates ta ci gaba da mamaye wasan, sai da kai ta sami damar zura kwallo ta hannun dan wasa Andile Jali, amma Ekramy ya hana kwallo shiga raga.

Za su kara a wasa na biyu a Alkahira ranar 10 ga watan Nuwamba, duk kungiyar da ta samu nasara, zakuma ta sami halartar buga gasar kungiyoyin zakarun Nahiyoyin duniya da za a fafata a watan Decemba a Morocco.