Arsenal na da jajircewa —Wenger

Image caption Wenger ya ce Arsenal za ta iya lashe manyan kofunan Turai

Arsenal ta nuna cewa ita kungiya ce da ke da jajircewa shi ya sanya ma ta lallasa Liverpool da ci 2-0 lamarin da ya ba ta karin maki 5 a Gasar Premier, in ji kocin kungiyar, Arsene Wenger.

Arsenal dai ta shiga wasan na ranar Asabar ne bayan da sau biyu tana shan kaye a wasannin da ta buga a gidanta --- wanda ta buga da Borussia Dortmund a Gasar Zakarun Turai da wanda ta kara da Chelsea a Gasar cin kofin League.

Wenger ya ce,"Yana da muhimmanci yadda muka buga wasan domin nuna wa mutane cewa za mu iya lashe wadannan manya Kofuna''.

A cewarsa, yadda suka doke Liverpool cikin sauki yana da matukar muhimmanci.

Karin bayani