Hart zai ci gaba da zaman benci

Joe Hart
Image caption Hart, zai sake hutawa a wasan kofin zakarun Turai

Golan Ingila Joe Hart zai ci gaba da zaman benci a gasar cin kofin zakarun Turai da Manchester City za ta kara da CSKA Moscow inji Manuel Pellegrini.

Hart ya zauna a benci ranar Asabar lokacin da suka kara a gida da Norwich City suka lashe wasan da ci 7-0 kuma Pantilimon ne ya kare raga.

Pellegrini ya ce Pantilimon dan kasar Romania zai ci gaba da kama wasa lokacin da zamu karbi bakuncin CSKA daga Rasha ranar Talata.

"ban san lokacin da Joe zai komo kama mana wasa ba, za dai mu ga me zamuyi nan gaba" inji Pellegrini.

Hart mai shekaru 26, ya sha fama da suka a manyan kura kuren da ya yi, na karshe shi ne wanda Chelsea ta lashe wasan da suka kara da ci 2-1 ranar 27 ga watan Oktoba.

Pellegrini ya kara da ce wa "yana da muhimmaci dan wasan ya huta, domin ya kama wasanni da dama na tsawon shekaru biyu da rabi.