Za a tuhumi shugaban Bayern Munich

Uli Hoeness
Image caption Hoeness da za a tuhuma kan kin biyan haraji

Shugaban Bayern Munich Uli Hoess zai bayyana a gaban kotu bisa tuhumar kaucewa biyan haraji.

Tsohon dan wasan Jamus ta yamma, ya bugawa Bayern wasa a shekara ta 1970 kafin ya zama mamba a hukumar kungiyar, shi ne kuma ya mika kansa ga mahukunta ya shaida musu cewa yana da asusun ajiya a asirce da bai sanar ba.

A watan Yuli ne dai masu shigar da kara suka tuhumi Hoeness mai shekaru 61 bayan binkice mai tsawo da suka gudanar.

Alkalan kotun jihar Munich sun ce za su fara sauraron shari'ar ranar 10 ga Maris, 2014.

Hoeness, wanda ya yi shekaru 30 a matsayin janar manajan Bayern kafin a zabeshi shugaban kungiyar, zai cigaba da rike mukaminsa.