Pirates ba ta fargabar shiga Masar

Pirates Al Ahly
Image caption Sai an je Alkahira za a sami zakaran bana

Kungiyar kwallon kafa ta Orlando Pirates ta shaidawa BBC ce wa ba ta damu da rashin tsaro a Alkahiraba ba, a shirye - shiryen da take na zuwa babban birnin na kasar Masar don karawa da Al Ahly a gasar cin kofin Zakarun Afrika.

Kungiyar Afrika ta kudu za ta kara da Al Ahly ne a filin wasa na Arab Contractors ranar Lahadi, a zagaye na biyu na gasar wadda ita ce irinta mafi girma ta zakarun Afrika, bayan wasa da suka tashi 1-1 a wasan da suka yi a Soweto ranar Asabar da ta gabata.

Rikicin Siyasa da tashin hankali a Masar, da kuma yawan samun yamutsi a wasan kwallon kafa, ya sa fargaba a zukatan 'yan wasa kuma sau biyu Ghana ta bukaci a dage karawar da za tayi da Masar a wasan shiga kofin duniya ranar 19 ga watan Nuwamba a Alkahira

Fifa ta amince a kara a Masar bayan da ta samu tabbaacin matakan tsaro daga gwamnatin Masar, Itama hukumar kwallon kafa ta AfriKa ta amince a buga wasan a Masar.