Fernando Torres zai yi jinya

Fernando Torres
Image caption Dan kwallon zai yi jinya bayan da ya dawo ganiya

Dan kwallon Chelsea Fernando Torres, ba zai buga wasanni biyu ba, sakamakon raunin da ya samu a kafarsa inji koci Jose Mourinho.

Dan kwallon mai shekaru 29, ba zai buga karawar da kungiyar zata yi da Schalke a gasar cin kofin zakaru da zasu kara ranar Laraba da kuma karawar da za su buga da West Brom a gasar Premier ba.

Dan wasan mai zura kwallo ba zai bugawa Spain wasan sada zumunci da zasu kara da Gabon ranar 19 ga watan Nuwamba.

Tsohon dan kwallon Liverpool ya dawo ganiyar sa bayan da ya zura kwallaye uku a bana.